Buhari ya gana da yarinyar da ta bashi gudunmawar kuɗi lokacin da yake yakin neman zabe


Shugaban kasa Muhammad Buhari, a yau Litinin ya gana da, Nicole Benson yarinyar  yar shekara 12 wacce ta bada gudunmawar kudin  kashewarta na makaranta ga yakin neman zabensa na shugaban kasa.

Benson na da shekaru 9 lokacin da ta bada gudunmawar kudin ga yakin neman zaben Buhari.

Da yake karɓar ta a fadar shugaban dake Abuja ya bayyana godiyarsa da gudunmawar da ta bashi.

Ya ce: ” ya kike? nagode sosai da gudunmawarki.”

Shugaban kasar ya kuma karbi bakuncin, Aisha Aliyu Gebi wata yarinya mai shekaru 10, yar asalin jihar Bauchi,da ta rubuto masa wasika tana neman sanin halin da lafiyarsa ke ciki.

A cikin wasikar ta ta Aisha ta bayyana kanta a matsayin babbar masoyiyar shugaban ƙasar inda yaya yake ji taji an ce bashi da lafiya dafatan yana samun sauki kana daga bisani ta nemi da a bata dama tazo ta duba shugaban kasar.

Har ila yau shugaban kasar ya gana da Maya wata yarinya yar shekara 3 wacce aka nadi fefan bidiyonta tana yiwa shugaban kasar addu’ar samun sauki. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like