Bola Ahmad Tinubu jagoran jam’iyar APC na kasa da kuma shugaban jam’iyar, John Odigie Oyegun na daga cikin mutanen da suka halarci wata liyafar cin abinci da shugaban kasa Muhammad Buhari ya shirya a ranar Laraba.
An fara taron liyafar da misalin karfe 8:30 na dare a babban dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa.
Bisi Akande, tsohon gwamnan jihar Osun, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Segun Oni, toshon gwamnan jihar Ekiti da kuma Kayode Fayemi,ministan tama da karafa na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Abiola Ajimo na jihar Oyo da kuma Tanko Al-makura na jihar Nasarawa.
Wasu yan majalisar kasa da suka fito daga yankin kudu maso yamma, ministoci da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyar APC na yankin duk sun halarci taron liyafar.
Taron da shugaban kasar ya kira bayan rasa nasaba da zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar cikin watan Yuli.