Shugaban kasa, Muhammad Buhari da kuma wasu manyan mutane na daga cikin wadanda suka halarci bikin yar gidan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
An dai gudanar da bikin a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Gwamnoni da dama da kuma wasu daga cikin yan majalisun tarayya suma sun halarci bikin.