Buhari Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Ginin Coci Ya Rufta Dasu A UyoShugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya aike da jaje tare da taaziyya ga al’ummar jihar Akwa Ibom kan rashin mutanen da aka yi sakamakon ruftawar coci a Uyo, ranar Asabar.
Buhari ya kuma taya gwamnan jihar da iyalinsa murna bisa tseratar da su da Allah ya yi daga ginin cocin da ya ruguje. Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu bayan da ginin cocin ya rufta a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.
A wata sanarwa da mataiamakin shugaban na musamman kan yada labarai, Garba Shehu, shugaba Buhari ya nemi al’umma da su agazawa mutanen da suka jikkata a hadarin.

Rahotanni dai sun ce Majami’ar Reigners Bible Church, ta cika makil saboda ana bikin nada shugabanta a matsayin Bishop a lokacin da lamarin ya faru.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato wadanda suka shaida lamarin na cewa ana kan yi wa ginin kwaskwarima saboda hasashen cewa jama’a da dama za su halacci taron.

Wani ganau ya ce “Ana cikin bikin nada Fasto Akan Week kwatsam sai ginin ya rufta baki daya”.

You may also like