Buhari ya jajantawa yan kasuwar kifi ta kano da gobara ta kona


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya jajantawa masu sana’a a kasuwar ƴan kifi ta Kano wadanda suka yi asara bayan da gobara ta kona  kasuwar.

Buhari ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu yafitar.

Shugaban kasar yace ya kadu matuka da samun labarin gobarar inda yace rahoton asarar wasu shaguna da kuma kontenoni dake kasuwar a bune mai tayar da hankali musamman ta bangaren tattalin arzikin mutanen da abin ya shafa.

A cewar shugaba Buhari, “wannan gobarar koma bayane  marar misaltuwa ga mutanen da gobarar ta shafa waɗanda suka yi asarar dukiyar da suka  dade suna tarawa.”

Haka kuma shugaban kasar ya jajantawa dukkanin al’ummar Kano kan gobarar inda yayi addu’ar Allah ya kare faruwar hakan anan gaba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like