Buhari Ya Kaddamar Da Manufofi Guda 7 Don Inganta Sashen Man Fetur


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar wasu manufofi guda bakwai domin inganta sashen man fetur da kuma iskar gas Nijeriya. Wasu daga cikin manufofin sun hada da samar da ci gaba a yankin Neja Delta da samar da tsaro a yankunan da ake hako mai da inganta matatun mai.
A yayin kaddamar da tsarin a jiya a Abuja, Shugaba Buhari ya ce har yanzu bangaren man fetur ya kasance babbar hanyar samun kudaden Nijeriya duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

An dai tsara shugaba Buhari zai gana da shugabannin al’ummomin yankin na Niger Delta mai arzikin mai a makon da za mu shiga.

Ministan mai na kasar Emmanuel Ibe Kachikwu, ya ce babbar manufar shirya ganawar ita ce, kawo karshen ayyukan tsagerenci da ke haddasa barna ga ayyukan man fetur wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar.

You may also like