Buhari ya kaddamar da rabon motocin noma a jihar Plateau


Shugaban kasa Muhammad Buhari,a a ranar Juma’a  ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Plateau.

A ranar karshe ta ziyarar tasa shugaban ya kaddamar da shirin rabawa manoma motocin noma da gwamnatin jihar ta samar.

Gwamnatin jihar karkashin shugabancin, gwamna Simon Lalong ce ta kaddamar da shirin a kokarinta na bunkasa harkar noma.

 A karakashin shirin manomin da ya mallaki motar zai biya kaso 60 na kudin gwamnatin jihar kuma ta biya kaso 30 ya yin da kananan hukumomi za su biya  kaso 10.

An samar da motocin noman kan kudi miliyan ₦1.4 ko wacce daya.

You may also like