Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Juma’a ya karbi bakuncin yan matan sakandaren Dapchi da aka sako a ranar Laraba.
An dauki yan matan a jiya Alhamis zuwa Abuja daga Maiduguri cikin wani jirgin saman soji.
A ranar Laraba ne ya’yan kungiyar ta Boko Haram suka dawo da yan matan garin Dapchi inda suka dauke su tun da farko.
Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Muhammad ya musalta jita-jitar da mutane wasu suke yadawa cewa gwamnati ta biya diyya kafin a sako yan matan.