Buhari ya karbi kasafin kudin shekarar 2018


Majalisar kasa ta mikawa shugaban kasa Muhammad Buhari kasafin kudin shekarar 2018 domin ya rattaba masa hannu ya zama doka kana a fara aiki da shi.

Ita Enang, babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, shine ya bayyana ga yan jaridar dake fadar shugaban kasa, ranar Juma’a.

“Na karbi kasafin kudin a madadin fadar shugaban kasa, yanzu zan mika shi,”ya fadawa manema labarai.

Da aka tambaye shi ina za akai kunshin kasafin kudin, Enang ya kara da cewa “Idan kasafin kudi ya baro gaban majalisa yana tafiya ne gaban shugaban kasa, shugaban kasa ya karbi kasafin kudin.”

Lokacin da ya jagoranci wasu yan majalisar kasa ranar Alhamis zuwa wurin buda baki a fadar shugaban, Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa ya fadawa manema labarai cewa za a mikawa shugaban kasa kasafin kudin a ranar Juma’a.

You may also like