Buhari ya kira Obasanjo


Shugaba Muhammadu Buhari ya kira tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ta wayar tarho daga birnin London don taya shi murna cikarsa shekaru 80 a duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana wa Cif Obasanjo cewa wannan wata dama ce da za a tuna irin gagarumar gudunmawa da Obasanjo ya rayu yana bayarwa don ci gaba da dorewar kasar nan, da dangantaka mai dorewa a fadin nahiyar Afrika dama duniya baki daya.

Haka, Shugaba Bugari ya tunawa tsohon Shugaban Kasar cewa irin su da suka yi aiki a karkashin Obasanjon a bangarori da dama, za su tuna cewa shi mutum haziki kuma mai kaifin tunani.

A karshe, Cif Obasanjo ya yi wa Shugaba Buhari fatan alheri da fatan samun ingantacciyar lafiya, tare da cewa yana daya daga cikin masu taya shi addu’a domin ya dawo gida ya ci gaba da ayyukan alherin da ya faro domin ci gaban Nigeria.

You may also like