Mataimakin shugaban kasa na musamman a shafin zumunta da kafofin watsa labarai, Femi Adesina ya sanar a shafinsa na Facebook cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira tsohon gwamnan jihar Ekiti, Niyi Adebayo daga Landan.
Kwanan nan tsohon gwamnan ya rasa mahaifinsa, tsohon kwamnan yankin Yamma, Manjo-Janar Adeniyi Adebayo.
Ga sakon da Adesina ya buga a kasa:
“A ranar Laraba shugabna kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi tsohon gwamnan yankin Yamma, Manjo-Janar Adeyinka Adebayo, a matsayin shugaba na gaskiya.
“A wani kiran tarho daga Landan zuwa gad an marigayin Janar kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Niyi Adebayo, shugaban kasar ya bayyana cewa tabbass Najeriya zatayi rashin rawar ganin da Janar Adebayo ya taka a kasar.
“Shugaban kasar ya kuma yi ta’aziyya ga mutanen jihar Ekiti da yan kabilar yarbawa gaba daya, tare da bayyana cewa marigayin ya jajirce gurin wanzar da hadin kai a kasar, ya kuma yi fada don ci gaban mutanen sa a matsayin shugaban kungiyar dattawan Yarbawa.
“Shugaban kasa yayi addu’an cewa Allah y aba iyalan Adebayo juriya ya kuma ji kan marigayin.
“Mista Niyi Adebayo, yayinda yake godiya ga shugaban kasa Buhari kan kiran da kuma ta’aziyyar, ya yi ma shugaban kasar fatan samun lafiya.”