Shugaba Muhammad Buhari ya koma Abuja bayan kammala ziyarar yini daya da ya kai jihar Kaduna inda ya kaddamar da wasu sabbin karagogin jirgin kasa da kuma tashar sauke kaya ta kasa da kasa ta farko a Arewa a yankin Kakuri a cikin jihar.
A yayin ziyarar, gwamnonin jihohin Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i da na Kano, Umar Ganduje ne suka mara masa baya, sai kuma Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da kuma Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris.