Buhari Ya Kori Wasu Shugabannin Hukumomin Sufurin Jiragen Sama



Shugaba Muhammadu Buhari ya kori hudu daga cikin shugabannin wasu hukumomin ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa, kuma ya maye gurbinsu da wasu nan take. 
Wadanda lamarin ya shafa sune; Manajan Daraktan NAMA Mista Emma Anasi, Babban Daraktan NIMET Mista Anthony Anuforom, Shugaban Makarantar Koyon Tukin Jirgin Sama dake Zaria Mista Samuel Caulcrick da kuma kwamishina mai kula da binciken hadurra.
Sanarwar ta ce a yanzu Fola Akinkoutu ya zama sabon shugaban NAMA, inda Sani Mashi zai jagoranci NIMET, yayin da Abdussalam Muhammed kuma zai shugabanci makarantar koyon tukin jiragen sama dake Zaria, haka kuma Mista Olateru zai kula da sashen kula da binciken hadurra.

You may also like