Buhari ya laƙabawa El-Rufai suna “Katafila”



Bayan da ya rushe ginin babban ofishin  tsagin jam’iyar APC da ke adawa da shi a Kaduna gwamna Nasir El-Rufai ya samu sabon lakabin suna “Katafila”.

Gwmnan ya samu wannan lakabin suna bada daga bakin kowa ba illa shugaban ƙasa Muhammad Buhari ranar Laraba lokacin taron majalisar koli ta ƙasa.

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta rushe gidan, Sulaiman Hunkuyi sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta arewa a majalisar dattawa.

Dan majalisar ya zargi El-Rufai da rusa masa gidansa ba bisa ƙaida sai dai ya ce a matsayinsa na mutum ya yafewa gwamnan.

Sai dai hukumar raya birane ta jihar Kaduna, KASUPDA tace ta rusa gidan ne saboda tunda fari an bayar da izinin gina shi a matsayin gida amma ba ofishin jam’iyar siyasa ba.

Mutane da dama zasu fassara wannan furuci na shugaban kasa a matsayin wani goyon baya kan abinda gwamnan ya aikata

You may also like