BUHARI YA RANTSAR DA MANYAN SAKATARORIN GWAMNATI GUDA BAKWAIShugaba Muhammad Buhari ya rantsar da wasu sabbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati su bakwai wadanda Mataimakinsa, Osinbanjo ya kaddamar da su a ranar 15 ga watan Agusta.

Manyan sakatarorin da aka rantsar sun hada da; Mustapha Sulaiman daga jihar Kano, Adekunle Olusegun Adeyemi daga jihar Oyo, Mrs. Ekaro Chukwumogwu daga jihar Rivers, Adedayo Apata daga jihar Ekiti, Abdulkadri Muazu daga jihar Kaduna, Osuji Ndubusi daga jihar Imo, sai Bitrus Nabasu daga jihar Plateau.

You may also like