Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Alkalan Nijeriya


justice-walter-onnoghen-600x409

 

A yau ne shugaban kasa Muhammadun Buhari ya rantsar da sabon shugaban alkalan Nijeriya CJN na wucin gadi, Mai Shari’a Walter Nkanu bayan da tsohon shugaban, Mahmoud Mohammad ya yi murabus.

An rantsar da shi a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 2:20 na ranar yau a gaban manya manya jami’an gwamnati na kasar nan.

Walter wanda dan asalin jahar Cross River ne zai rike mukamin na tsahon watanni uku, Kafin shugaban kasar ya zabi sabon shugaba, majalisa kuma ta amince da zabin.

A jiya Laraba da daddare ne wa’adin aikin tsohon shugaban Mahmoud Muhammad ya cika, yayin da ya cika shekaru 70 a yau Alhamis.

You may also like