Shugaba Muhammad Buhari ya roki Shugabannin al’ummomin jihar Binuwai kan su wayar da kan mabiyansa kan kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta shawo kan rikicin makiyaya da manoma a jihar.
Shugaban wanda ya kai ziyara a Binuwai a yau, ya kuma nemi Shugabannin jihar kan su guji dabi’ar mayar da martani kan wani hari da aka kai masu ta yadda jami’an tsaro za su samu damar gudanar da ayyukansu.
Ya kara da cewa ya yi matukar mamaki kan yadda Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ki bin umarninsa na komawa cikin jihar bayan kisan da makiyaya suka yi a kan wasu manoma 73.