Buhari Ya Sake Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Dawo Da Sauran ‘Yan Matan Chibok Gida


4bka3ee7476c13g15d_800c450

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinta ta kwatowa da kuma dawo da sauran ‘yan matan makarantar Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace su daga makarantarsu da ke garin Chibok din a jihar Borno sama da shekaru biyun da suka gabata.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yau din a yayin da ya ke ganawa da ‘yan matan Chibok din su 21 da aka sako su a kwanakin baya inda ya taya iyayen yaran murnar dawowar wadannan ‘ya’ya na su da kuma alkawarin ci gaba da kokari har sai an sako sauran yaran da suka rage din.

A cikin jawabin nasa, shugaba Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta dau nauyin kula da lafiya da kuma rayuwar ‘yan matan, kamar  yadda ya ce gwamnatin za ta dauki nauyin karatunsu da kuma ayyukan da suke son yi a rayuwa, yana  mai cewa har ya zuwa yanzu dai ‘yan matan ba  su makara ba  wajen ci gaba da karun na su.

Har ila yau shugaban na Nijeriya ya yaba da kuma jinjinawaiyayen yaran saboda irin hakuri da juriyar da  suka nuna tsawon lokacin da ‘ya’yan na su suke tsare a  hannun ‘yan Boko Haram din, kamar yadda kuma ya gode wa ‘yan Nijeriya da kuma  sauran kasashen duniya saboda goyon bayan da suka ba wa gwamnatin nasa da kuma rashin yanke kauna daga irin kokarin da take yi na kwato ‘yan matan, kamar yadda kuma ya gode wa jami’an tsaron kasar saboda namijin kokarin da suka yi a wannan bangaren.

A makon da ya wuce ne dai kungiyar Boko Haram din ta sako ‘yan matan su 21 bayan wata tattaunawa da ta gudana tsakaninsu da gwamnatin Nijeriyan bisa sanya ido da shiga tsakanin kasar Swiss da kungiyar Red Cross ta  duniya.

You may also like