Buhari Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kudin 2023
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2023.

Kasafin kudin na bana, wanda ya samu karin naira tiriliyan 1.32 zai lakume naira tiriliyan 21.83.

A baya, fadar shugaban kasar ta tsara kasafin kudin na bana akan naira tiriliyan 20.51.

Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin ne yayin wani biki da aka yi a fadarsa a ranar Talata a Abuja.

Bikin sanya hannu kan kasafin kudin na bana ya samu halartar shugabannin majalisun dokokin kasar.

A makon da ya gabata majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudin.

Shugaban na Najeriya wanda ke shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu, ya ce, ya sanya hannu kan kasafin kudin ne don a fara aiwatar da shi ba tare da bata lokaci ba.Source link


Like it? Share with your friends!

4

You may also like