Buhari Ya Sanya Ranar Da Zai Bayyana Gaban Majalida Don Gabatar Da Kasafin KudiShugaba Muhammad Buhari ya sanya ranar 14 ga watan Disamba a matsayin ranar dai zai bayyana gaban zaurukan majalisar tarayya don yi masu cikakken bayani game da kasafin kudin 2017.
A cikin wasika da ya aikawa majalisar wanda kuma Shugaban Majalisr Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya karanta a gaban ‘yan majalisa, Shugaba Buhari kuma ya nuna zai yi majalisar bayani kan shirye shiryen da ya tanada don farfado da tattalin arzikin Nijeriya. A makon da ya gabata ne, majalisar ministoci ta amince da kasafin wanda aka tsara kashe Naira Tiriliyan 7.02.

You may also like