Shugaban kasa Muhammad Buhari tare dq yan tawagarsa sun isa birnin Paris na ƙasar Faransa domin halartar wani taro na kasashe 50 kan sauyin yanayi.
Shugaban wanda ya samu rakiyar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredelu da kuma na jihar Adamawa Jibrila Bindow.
Shugaban ya tashi daga birnin Kano bayan da yayi hutun karshen mako a mahaifarsa ta Daura.