Shugaban kasa Muhammad Buhari ya isa Katsina akan hanyarsa ta zuwa Daura mahaifarsa domin ziyara.
Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa Yar’adua da misalin ƙarfe 4:30 na rana.
Buhari ya samu tarba daga gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari tare da manyan mukarraban gwamnatinsa, Shugabannin hukumomin tsaro da kuma masu riƙe da masarautun gargajiya.
Bayan ya gama gaisawa da mutane shugaban ya shiga jirgi mai saukar ungulu mallakin rundunar sojin saman Najeriya da ya ɗauke shi zuwa Daura.
Ana sa ran ya yin ziyarar tasa shugaban zai gana da ƴan uwansa da kuma yin ta’aziyar yan uwansa biyu da suka mutu Aisha Mamman da kuma Halima Dauda.