Shugaba Muhammad Buhari ya yi alwashin ganin cewa mayakan Boko Haram sun sako dalibar makarantar Sakandaren Dapchi, Leah Sharibu da mayakan Boko Haram suka ki sakinta bayan sun dawo da sauran dalibai 104 da suka arce da su kwanaki.
Haka nan kuma, iyayen dalibar sun roki gwamnatin tarayya kan ta jajirce wajen ganin an sako masu diyar su ‘yar shekara 15, Mayakan Boko Haram dai sun yanke shawarar kin Sakin dalibar ce saboda ta ki karbar addinin Musulunci.