Buhari Ya Shiga Rikicin Tinubu Da Shugaban APC


Shugaba Muhammad Buhari ya shigo cikin rikicin da ya barke tsakanin Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu da kuma Shugaban APC na kasa, Cif Oyegun bayan da Tinubu ya zargi Shugaban jam’iyyar da gurgunta aikin da Buhari ya bashi na sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da ke rigima da juna.

A jiya ne, Buhari ya gayyaci Shugaban APC inda suka yi zama na kusan awa guda wanda bayan tattaunawar ce ya fitar da wani jawabi na yin raddi ga wasikar da tsohon Gwamnan Legas din ya zarge shi da lalata masa aiki. Sai dai kuma maimakon ya amsa korafe-korafen da Tinubu ya zayyano a cikin wasikar sa Oyegun ya bige da yi wa Tinubu fatan Alkhairi ne kan aikin sasanta rikicin jam’iyyar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa shi ya yi.

You may also like