Buhari ya tafi kasar Chadi don halartar bikin rantsar da Deby


 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tashi zuwa Ndjamena babban birnin kasar Chadi domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Idris Deby Itno.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta bayyana cewa, Buhari zai dawo gida Najeriya bayan an kammala bikin rantsuwar.

An sake zabar Idris Deby a zaben da aka gudanar a watan Afrilun da ya gabata.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Gnaduje da na Borno Kashin Shettima ne suka raka shugaba Buhari zuwa Chadin.

Haka zalika a tawagar shugaban akwai sanatoci 2 Baba Kaka Garba da Tahir Monguno da kuma ministan harkokin waje na kasar Geoffrey Onyeama da mai bawa shugaban shawara jkan sha’anin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

You may also like