Buhari ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban kasar Laberiya murna Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a ranar Juma’a  ya miƙa sakon taya murna ga sabon shugaban ƙasar Laberiya, George Weah kan nasarar da ya samu azagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina yafitar, Buhari ya  yabawa mutanen ƙasar Laberiya kan yadda suka yi zaben mai dinbin tarihi ba tare da tashin hankali ba.

 Haka kuma Buhari ya yabawa hukumar zaɓen ƙasar ta Laberiya da kuma masu sanya idanu a zaɓen na yankin Afrika ta yamma dama na  duniya baki daya wadanda suka bada gagarumin gudummawa wajen karfafa dimakwaradiya a ƙasar ta yankin yammacin a Afrika.

Shugaban kasar ya bayyana nasarar ta Weah a matsayin manuniya dake tabbatar da kudirin yan kasar na cigaba da zama tare cikin zaman lafiya da yalwar arziki.

Har ila yau shugaban ya yabawa shugaba mai barin gado, Ellen Johnson Sirleaf kan cigaban da ta kawowa kasar cikin shekaru 12 da ta kwashe tana mulkin ƙasar da kuma dattakon da ta nuna wajen gudanar da zabe mai cike da adalci.

Wannan ne dai karo na farko cikin shekaru 73 da wani shugaba zaɓaɓɓe yake miƙa mulki ga wani da aka zaba a kasar ta Laberiya.

You may also like