Buhari Ya Tsani Masu Kudi Da ‘yan Siyasa – Tony Anenih “Lokacin da Buhari yayi mulki a matsayin Soja ya daure ni tsawon wata 8 tun daga watan Maris na 1984 zuwa Augusta na 1985 saboda kawai Nine Shugaban Jam’iyar NPN. Bayan haka kuma yayi ta kama yan siyasa yana tura su gidan kurkuku ba gaira ba dalili”.
Tsohon shugaban Kwamatin Amintattu Na Jam’iyar PDP Chief Tony Anenih ya fadi hakan ne acikin wani litafinsa da rubuta na rayuwarsa a Siyasa
Chief Tony Anenih ya kuma ce Shugaba Buhari tare da Tunde Idiagbon sun kama shi sun gargame shi a gidan kurkuku saboda kawai yana da kudi da kuma cewar shine shugaban jam’iyar NPN.

You may also like