Fadar shugaban Nijeriya ya sanar da cewa shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya tura wata tawaga ta manyan jami’an gwamnatin kasar zuwa jihar Borno don isar da jaje da iyalai da ‘yan’uwan mutanen da wani hari bisa kuskure da jiragen yakin sojin sama na Nijeriyan suka kai wa wasu ‘yan gudun hijira da suke sansanin ‘yan gudun hijiran da ke Rann kusa da kan iyakar kasar da Kamaru.
A wata sanarwa da kakakin shugaban Nijeriya Femi Adeshina ya fitar ya ce tawagar wace take karkashin shugaban Ma’aikata na fadar shugaban kasar ne Abba Kyari ta hada da ministocin tsaro da na watsa labarai, babban hafsan hafsoshin sojan Nijeriya, bugu da kari kan manyan hafsoshin sojin kasa da na sama na kasar.
Tuni dai tawagar ta gana da gwamnan jihar Bornon Kashin Shettima inda suka isar masa da ta’aziyyar shugaba Buhari dangane da wannan kuskure da ya faru da kuma jaddada shirin gwamnatin Tarayyar na taimaka wa wadanda abin ya ritsa da su. Haka nan tawagar ta kai wa sarkin Dikwa Alhaji Abba Tor Shehu masta II, babban asibitin kwararru na Maiduri da kuma cibiyoyin ba da agaji da suke Maidugurin don isar da sakon ta’aziyyar da kuma ganin halin da wadanda suka sami raunuka suke ciki.
A jiya Talata ce dai sojojin sama na Nijeriya suka kai hari bisa kuskure kan sansanin ‘yan gudun hijira da ke kauyen Rann a karamar hukumar Kale-Balge da ke jihar Borno; bisa tunanin ‘yan Boko Haram ne wadanda suke sansani a wajen lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 52 da kuma raunana wasu sama da 120.