Buhari ya umarci Babban Sifetan Yan’sanda ya koma jihar Benue


Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya umarci babban sifetan yan’sanda na ƙasa Ibrahim Idris da ya koma jihar Benue domin dawo da doka da oda da kuma  hana kara kisan rayukan mutane.

Jimoh Mashood, mai magana da yawun rundunar yace umarnin ya biyo bayan kisan mutanen da aka yi  a kananan hukumomin Guma da kuma Logo.

Mashood yace domin bin umarnin shugaban kasa, babban sifetan  zai tafi da ƙarin rukuni 5 na  jami’an yan sandan kwantar da tarzoma domin cikewa su zama rukuni 10 da aka tura jihar.

Ya ce sauran rukunin jami’an yan’sanda da tuni aka tura jihar za su cigaba da aikinsu na sintiri da kuma hana faruwar aiktalaifuka a wuraren da aka kai harin.

Mai magana da yawun rundunar yayi gargadin cewa rundunar baza tayi kasa  a gwiwa ba wajen hukunta duk wasu fitinannun rukunin mutane ko kuma ɗai-ɗai ku da ka iya yin duk wani abu da zai sake rura wutar rikicin.

You may also like