Mai ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin kafafen yada labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa ya yi magana da shugaban kasa nan ba da jimawa ba. Adesina ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya kara da cewa shugaban kasar ya ce jama’a su kwantar da hankali ba wani abin daga hankali ya na hutawa ne kawai.