Buhari ya yi Allah wadarai da kisan Deborah | Labarai | DWIta dai daliba Deborah Samuel, ta fuskanci bugu da jifa da duwatsu daga dandazon daliban makarantar, kana daga bisani suka kone gawarta bayan da ta mutu. A wata sanarwar da ya fitar shugaban na Najeriya kasar da ta fi kowace a nahiyar Afirka yawan al’umma, ya ce ba wani dan kasar da ya isa ya yiwa kansa shari’a.

Kafin kiran na shugaban Najeriya shi ma mai alfarma sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci mutanen yankin da su zauna lafiya, bayan da yayi Allah wadarai da kisan dalibar.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin ‘yan sanda a wannan jihar da ke kan turbar kwarya-kwaryar shari’ar Muslunci, sun ce sun kama akalla mutun da ake zargi na da hannu wajen tayar da fitinar, kana nan ba da jimawa ba ana shirin gurfara da su a gaban kotu. You may also like