Shugaban kasa,Muhammad Buhari a ranar Talata ya yi wata ganawar sirri da jagoran jam’iyar APC na kasa, Bola Ahmad Tinubu, a birnin Landan.
Mai bai wa shugaban kasar shawara kan kafafen sadarwar zamani,Bashir Ahmad shi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter @BashirAhmad.
Mai taimakawa shugaban kasar ya rubuta: ” shugaban kasa Muhammad Buhari ya karbi bakuncin jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yau a birnin Landan.”
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa Buhari wanda ke ziyarar aiki a birnin Landan, a ranar Laraba ne ya gana da Akbishop na Canterbury, Justin Welby inda ya bayyana masa dalilinsa na son sake tsayawa takarar shugaban kasa.