Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce Shugabannin kasashen Afirka dole ne suyi magana da murya guda ” ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba,” domin cimma hadib kai ta fannin tattalin arziki, cigaba, zaman lafiya, da kuma tsaro a nahiyar.
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu shine ya jiyo Buhari na fadin haka a wata tattaunawa da shugaban kasar Guinea Alpha Conde a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Shugaban kasar ya shawarci shugabannin da su koyi daga irin abubuwan da suka faru a baya wajen magance rikice-rikice, tsatsauran ra’ayi,da kuma bazuwar kananan makamai.
Dukkanin shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen biyu.
Ya tabbatarwa da takwaransa na kasar Guinea wanda shine shugaban tarayyar Afirka cewa Najeriya za ta cigaba da tattaunawa da dukkanin mambobin kungiyar ta AU domin maganin matsalolin tsaro a ƙasashe irinsu, Sudan ta Kudu, Libiya da kuma rikicin siyasar kasar Togo.
Ana sa jawabin shugaba Conde ya yaba da rawar da Najeriya take takawa a nahiyar, musamman namijin kokarin da shugaba Buhari ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa.