Shugaba Muhammad Buhari ya yi sabbin nade-nade na shugabannin wasu hukumomin gwamnati wanda ya hada har da Kwamishinonin zabe.
Wadanda aka nada sun hada da Dakta Abdulkarim Yusuf a matsayin daraktan asibitin masu tabin hankali da ke Kaduna, sai Dakta Abubakar Musa, daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Nguru, Dakta Abdullahi Ibrahim, daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Azare.
Sai Dakta Illiasu daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Owo sauran su ne, Dakta Nasir Umar Shugaban cibiyar NOFC da ke Bauchi Dakta Aliyu Ladan, Shugaban cibiyar NOFC, da ke Katsina, Dakta Stella, Babbar manajar Gidan Wasanni da ke Legas, Dakta Baba Danjuma Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Idah.
Sai kuma Dakta Usman Kallamu, Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Damaturu, Dakta Jimah Sanusi, Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Auchi, Dakta Dayo Oladebeye, Shugaban kwalejin Kimiyya da ke ado-Ekiti, Sanusi Gumau, Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Bauchi, Farfesa Tomunomi Abbey, Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Bonny.
Sai Faruk Haruna a matsayin Shugaban kwalejin horas da malamai ta Kontagora, Omokungbe Omoseni, Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Yaba, sai kuma Emmanuel Alex Hart, Mohammed Magaji Ibrahim, Dr. Cyril Omorogbe, Dr. Uthman Abdulrahman Ajidaba, Mr. Segun Agbaje, Baba Abba Yusuf da Yahaya Bello a matsayin kwamishinonin zabe.