Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Isyaka Rabi’u


Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana rasuwar Alhaji Isyaku Rabi’u a matsayin babban rashi ga duniyar ilimin addini da kuma na kasuwanci inda ya jinjinawa marigayin kan irin gudunmawar da ya bayar wajen tallafawa harkar ilimi tare da samar da dimbin ayyukan yi ta hanyar zuba jari a harkoki daban daban.

Shugaba Buhari ya bayyana Marigayi Isyaka Rabi’u ya samu nasarorin rayuwa ce bisa sanya gaskiya cikin harkokinsa inda ya kalubalanci ‘ya’yan marigayin kan su yi koyi da mahaifinsu tare kuma da dorewa kan manufofinsa inda ya yi masa fatan samun rahamar Ubangiji.

You may also like