Buhari ya yi watsi da gyaran dokar zabe da majalisun tarayya su ka yi


Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya yi watsi da  gyaran dokar zabe da majalisar kasa ta yi. Dokar wacce ta tanadi sauya tsarin jadawalin zabukan shekarar 2019.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa shugaban kasar ya bada hujjoji uku da suka saka shi kin amincewa ya rattaba hannu akan kudurin dokar wacce dukkanin majalisun tarayya suka amince da ita.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa shugaban kasar ya sanar da matakin nasa cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma  kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Ana sa ran shuwagabannin majalisun biyu za su karantawa abokanan aikinsu abin da wasikar ta kunsa a ya yin zaman majalisun a tsakanin ranar Talata  zuwa Alhamis.

Bayan amincewa da gyaran dokar da majalisun suka yi, manyan lauyoyi, kungiyoyin farar hula da kuma wasu  d’ai-d’aikun mutane sun nuna adawarsu da gyaran dokar.

You may also like