Buhari ya zaɓi Tinubu a matsayin wanda zai sasanta rikicin jam’iyar APC


Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya zaɓi Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda zai sasanta rashin jituwar dake faruwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar APC.

Garba Shehu babban mai taimakawa shugaban ƙasa Muhammad Buhari kan harkokin yaɗa labarai ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.

Tinubu jagoran jam’iyar na ƙasa zai shirya tsakanin yan jam’iyar da kuma buɗe kafar da za ta kawo sasantawa.

Sanarwar ta ce ” a ƙoƙarin da ake na karfafa haɗin kai a jam’iyar APC shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya zaɓi Bola Ahmad Tinubu ya jagoranci tuntuɓa da kuma sasantawa.

“Aikin da aka bashi ya haɗa da warware rashin fahimta a tsakanin ƴan jam’iyar, shugabannin jam’iyar, da kuma wasu masu riƙe da muƙaman siyasa  a wasu jihohin.”

You may also like