Buhari ya ziyarci makarantar yan mata dake Dapchi


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ziyarci makarantar sakandaren Yan Mata ta Kimiyya Da Fasaha dake Dapchi a jihar Yobe inda yayan kungiyar Boko Haram suka sace yan mata 110 cikin watan da ya wuce.

Ya samu rakiyar Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe wanda tun farkon faruwar lamarin ya ziyarci makarantar.

Garin Dapchi nan ne hedikwatar karamar hukumar Busari ta jihar Yobe.

Shugaban kasar ya ziyarci makarantar ne biyo bayan suka da ya sha daga wurin yan adawa kan kin ziyartar garin da ya yi tun bayan sace yan matan.

You may also like