Buhari Yana Da Koshin Lafiyar Tsayawa Takara A 2019 – Kawu Sumaila 


Mai baiwa Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar wakilai,  Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila, yace mai gidansa Shugaban kasa Muhammad Buhari yana da koshin lafiyar da zai iya tsayawa takara, a shekarar 2019.

Sumaila ya bayyana haka ne a jiya Litinin, lokacin da yake ganawa da yan jaridu a gidan gwamnatin jihar Kano, yace rahoton likitoci ne kawai zai iya hana shugaban sake neman tsayawa takara a karo na biyu.

A tabakinsa babu abin damuwa kan rashin lafiyar Shugaban, domin tun kafin zaben 2015 ake yada jita-jita kan rashin lafiyar Shugaban.

Yace wasu mutane da basa san kasarnan da alkhairi, sune ke yada labarai marasa dadi akan lafiyar shugaban. 

“Ina da tabbacin cewa Buhari yana da koshin lafiyar da zai iya tsayawa takara , shekarun Buhari 74, kuma rashin lafiya ga dattijo mai irin wannan shekaru ba abu ba ne bako.

“sai dai idan likitocinsa sun bada rahoton cewa  bazai iya neman takara ba a karo na biyu,idan ba haka ba, babu ja da baya a yunkurin sa na tsayawa takara  a 2019”

Tsohon dan majalisar tarayyar yace babu wani da dantakara da zai tsorata Buhari. 

You may also like