Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da tsohon Shugaban Goodluck Jonathan ya kasa yi a tsawon mulkinsa.
Tinubu ya fadi hakan ne a jawabinsa a Kwalejin Tsaro da ke Abuja.
Tinubu ya kuma jinjinawa sojojin Nijeriya akan nasarorin da suka samu a yaki da Boko Haram.
Bayan haka kuma ya kara jinjinawa shugaban kasa akan rashin takura wa gidajen jaridu da gwamnatinsa ba sa yi da kuma walwala da aka samu a harkar.
Daga karshe ya ce jam’iyyar sa ta APC za ta cigaba da samar da ingantattun ayyuka domin mutanen Nijeriya kamar yadda ta yi alkawari.