Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Da Wasu Yan Bindiga Suka  Kai Wata Coci A  Anambra Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai wata majami’a dake jihar Anambra.

Buhari a wata sanarwa da yafitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu, ya bayyana harin a matsayin a wani abu mai muni da bai dace ba akan bil’ama.

Shugaban kasar ya bayyana damuwar kai harin, inda yace ” Babu wani dalili kowanne iri da zai sa akai hari  kan masu Ibada cikin cocin tare da kashe su cikin ruwan sanyi.”

 Shugaban ya jajantawa iyalan wadanda suka rayukansu, shugabannin cocin da kuma gwamnatin jihar Anambra.

Ya kuma tabbatarwa da yan Najeriya kokarin gwamnatinsa na kare dukiyoyinsu da rayukansu a koda yaushe kuma a ko ina suke. 

You may also like