Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabanni Musulmi da kungiyoyin kasa da kasa wajen yin Allah-wadai da harin da aka kai da makami mai linzami kan garin Makkah.
Kanfanin Dillacin Labarai na Saudiyya, wato Saudi Press Agency (SPA) ya ruwaito cewa Shugaba Buhari ya kira Sarki Salmanu dan AbdulAziz Alu Sa’ud, inda bayan ya jajanta masa mugun nufin da aka nufi garin na Makkah, ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da tsare garin Makkah da tsarewar sa da dukkan Musulmi.
Shi ma Sarki Salman ya roki Allah Ya taimaki Nijeriya Ya kai ta ga cin nasara, Ya kuma kareta daga sharrin makiya.