Buhari YaYi Martani Akan Kin Karbar MukamansaFadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce shugaban kasar ba ya tura wa majalisar dattawa sunayen mutanen da yake so a nada musu mukami a gwamnatinsa, sai ya bi dukkan hanyoyin tuntuba.

Fadar dai tana mayar da martani ne dangane damatakin da wasu daga cikin mutanen da aka mika wa majalisa sunayensu suka dauka na kinkarbar tayin aiki da gwamnatin Buharin kan, lamarin da ya sa masana zargin cewa gwamanti na ayyana sunayen ne ba tare da tuntuba ba.

Malam Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai, ya shaida wa BBC cewa masu cewa ba a tuntube su ba, suna kokari ne su shafa wa gwamnati kashin-kaji kawai.

Ya ce game da Uwargida Paulin Tallen daga jihar Filato, jinkiri aka samu na dan sakon da gwamnati ta tura mata har aka yi sanarwar, shi kuwa Dakta Usman Bugaje, kakakin ya ce ya gaya musu a shirye yake ya yi aiki da gwamnatin, amma kuma ya riga ya karbi wasu ayyuka a kasashen waje, da ba zai yiwu ya hada biyun ba.

You may also like