Buhari Zai Bude Taron Tallalin Arziki Da Tsaro Na Yankin Kudu Maso GabasA ranar 22 ga watan Disamba ne aka tsara Shugaban Kasa, Muhammad Buhari zai ziyarci jihar Enugu don bude taron tattalin arziki da tsaro na jihohin Kudu maso Gabas. 
Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya ya ruwaito cewa Shugaba Buhari ya amince da halartar taron ne saboda kaunar zaman lafiya da ci gaban yankin na Kudu maso Gabas.

 Taron dai zai tattauna yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin ne sai kuma samar da yanayin bunkasar Harkokin tattalin arziki.

You may also like