Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu sauki sosai a lokacin da ya ziyarceshi a makon da ta gabata a London.
Kalu ya bayyana cewar shugaban kasar zai iya dawowa gida kafin ranar 11 ga wannan watan, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su nisanci yada jita-jita ta kiyayya game da lafiyar shugaban kasar wanda ya ce a halin yanzu ya samu sauki.
Yayin da yake magana a cikin wata hira a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas, Kalu ya ce abin takaici ne ganin yadda wasu ‘yan Najeriya ke yada karyan jita-jita game da lafiyar shugaba Buhari maimakon yi masa addu’ar samun sauki ya koma bakin aikin sa.
Kalu ya ce ya ziyarci birnin Landanne musamman don ya duba lafiyar shugaba Buhari.
Ya ce:”Na tafi Washington don na ziyarci abokan kasuwanci na kuma daga can na biya Landan don ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu yana murmurewa sosai.”
“Na yi farin ciki yadda na samu shugaba Buhari duk da sakonnin kiyayya da wasu mutane ke yadawa game da shi.
“Amma kuma ina bakin ciki game da maganganu na kiyyaya da wasu ‘yan Najeriya ke fada game da lafiyar shugaban don na gane wa ido na yadda shugaban kasar yake.”
A wani bangare kuma tsohon gwamnan ya ce ya yabawa shugaba Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma durkushe ‘yan ta’addan Boko Haram.