Buhari zai halarci taron cigaban Afrika da za a yi a kasar Japan


Shugaban kasa Muhammad Buhari zai tashi daga filin jirgin saman Abuja ranar Lahadi ya zuwa kasar Japan domin halartar taron kasa da kasa kan cigaban Afrika karo na bakwai da akaiwa lakabi da TICAD7.

Taron zai gudane ne a birnin Yokohoma daga ranar 28 ya zuwa 30 ga watan Agusta.

A wata sanarwa ranar Juma’a mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce wannan ne karo na biyu da Buhari zai halarci taron bayan da ya halarci TICAD6 da aka yi a Nairobi babban birnin kasar Kenya cikin watan Agustan shekarar 2016.

Adesina ya ce firaministan kasar, Shinzo Abe shine zai bude taron.

A yayin ziyarar shugaban kasa zai samu rakiyar wasu gwamnoni da suka hada da Babagana Umara Zulum na jihar Borno,Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos,da kuma Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara.

You may also like