Buhari zai halarci taron MDD a New York


 

2016-02-03t122339z_640608810_lr1ec230yf47x_rtrmadp_3_france-politics1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin shugabanin kasashen duniya da za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kashi na 71 a birnin New York, in da zai gana da wasu daga cikin shugabanin kan matsalar tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

Fadar shugaban ta ce, Buhari zai kuma tattauna kan yadda za a sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, tare da magance matsalar ta Boko Haram da ta Naija Delta.

Shugaban wanda zai kwashe kwanaki biyar yana halartar taruka daga ranar Litinin 19 ga watan Satumba zuwa Juma’a 23 ga watan, zai yi jawabi a babban zauran Majalisar Dinkin Duniya, kana ya sanya hannu akan yarjejeniyar kare muhallin da aka kulla a Paris.

Mai Magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya ce, Buhari zai kuma jagoranci wani taron bunkasa kasuwanci tsakanin shugabanin Afrika da Amurka da wani taro na daban da cibiyar Clinton ta shirya, kana da wani taron Majalisar Dinkin Duniya kan muradun jama’a da Sakatare Janar ke shirya wa.

You may also like