Buhari zai je duba lafiyarsa a London | Labarai | DWMai shekaru 78 da haihuwa, Buharin ya sha yin irin wannan balaguro don duba lafiyarsa a kasar ta Birtaniya, tun bayan hawan sa mulki a shekara ta 2015, duk da korafe korafe daga bangaren al’ummar kasar.

A watan Maris ne dai shugaban Najeriyar ya kai ziyara makamancin wannan a birnin London, tafiyar da yayi gabanin yajin aikin likitocin Najeriyar, saboda rashin isassun kayan aiki da albashi mai inganci.You may also like