A gobe Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bikin aza tubalin ginin layin dogo daga Kano zuwa Maradi, wanda aka bayar a kan dala biliyan biyu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya sanar da haka ta shafinsa na twitter, ya ce za a bude aikin ne a yankin Katsina.
A watan Janairun 2021, Gwamnatin Tarayya ta shiga yarjejeniyar aiki tare da Kamfanin Mota-Engil kan aikin layin dogo tsakanin Kano zuwa Maradi da zai ci dala biliyan 1.959.