Buhari zai kai ziyara Yola ranar Talata


Shugaban ƙasa Muhammad Buhari zai kai ziyara Yola babban birnin jihar Adamawa a ranar Talata.

Yayin ziyarar tasa ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da wasu aiyuka kana ya gabatar da jawabi a wurin babban taron da jihar ta shirya kan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Martins Babale mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin tsare-tsare kan ziyarar ya ce an kammala dukkanin wasu shirye-shirye da suka kamata na tarbar shugaban.

“Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya amince ya zo  ya bude taron da kansa lallai wannan wani abun tarihi ne ga jihar Adamawa dama Najeriya baki ɗaya,”Babale ya ce.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa shine zai jagoranci gabatar da makala a wurin taron.sauran masu gabatar da maƙala sun haɗa da Ibrahim Mustafa Magu shugaban hukumar EFCC da kuma Bolaji Owosanaye shugaban hukumar hana ci da karɓar rashawa ta ICPC.

Rundunar ƴan sandan jihar ta sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa a wasu tituna dake jihar.

Othman Abubakar mai magana da yawun rundunar yace an ɗauki wannan mataki ne domin bawa motocin shugaban ƙasa damar wucewa ba tare da tsaiko ba.

You may also like